
Manjo-Janar Emeka Onumajuru ya bayyana cewa sojojin suna kan bibiyar motsin Bello Turji, kuma sun gano inda yake, amma bai yi ƙarin bayani ba.
Babu wani kwan-gaba-kwan-baya a wurin sojoji kan maganar Bello Turji, mun gano inda maɓoyarsa take,” in ji Janar Emeka.
Ya ci gaba da cewa a halin yanzu sojoji sun riga sun rutsa Turji a maɓoyarsa, babu inda zai iya motsawa ya je, saboda tsoro.
Ya bayyana haka ne a safiyar Litinin yana mai cewa kwanakon Turji sun kusa karewa.
Janar din ya bayyana haka ne a yayin hirar da gidan talabijin na Channels ya yi da shi a ranar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI