Mun cafke ƴan kwaya sama da dubu 18 a Najeriya - Buba Marwa

Mun cafke ƴan kwaya sama da dubu 18 a Najeriya - Buba Marwa

Marwa ya faɗi haka ne a yayin kaddamar da wani sabon ofishin hukumar ta NDLEA a shalkwatarsa da ke birnin Lagos a wannan Talatar.

Sabon ofishin wanda gwamnatin Amurka ta bai wa NDLEA gudunmawarsa, zai rika tattara da kuma tantance hujjoji kan miyagun kwayoyin da aka kama.

Marwa ya jinjina wa Amurka kan irin gudunmawar da take bai wa hukumar ta NDLEA wajen yaƙi da ta'ammuli da muggan kwayoyi a sassan Najeriya.

A yau, ina cike da farin cikin gudunmawar Amurka, musamman ta wannan babban ofishin na tattara hujjojin ta'ammulli da kwayoyi.

Wannan ofishin na da matukar muhimmanci wajen tattara hujjojin da za su sauƙaƙa gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata laifukan da ke tattare da ta'ammuli da muggan kwayoyi.

Lokacin da shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa ke ƙaddamar da sabon ofishin tattara hujjoji kan kwayoyi da Amurka ta bai wa hukumar gudunmawa a birnin Lagos. Lokacin da shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa ke ƙaddamar da sabon ofishin tattara hujjoji kan kwayoyi da Amurka ta bai wa hukumar gudunmawa a birnin Lagos. © Abdurrahman Gambo/RFI Hausa (08/12/2023)

Kodayake duk da kokarin da hukumar NDLEA ke yi na magance matsalar safarar kwayoyi a Najeriya, amma Marwa ya ce, akwai sauran rina a kaba domin kuwa babu alamun kawo karshen wannan matsalar nan kusa a cewarsa.

Shugaban na NDLEA ya ce, za su ci gaba jajircewa don ganin sun shawo kan matsalolin da suke fuskanta a matsayinsu na hukuma.

Daga cikin mutane sama da dubu 18 da 500 da hukumar ta NDLEA ta cafke a bara, an gurfanar da dubu 3 da 250 a gaban kotu da suka haɗa da mutane 10 da ke zama gaggan masu safarar kwayoyi a Najeriya.

A ɓangare guda, NDLEA ta ce, ta yi nasarar sauya wa mutane dubu 8 da 200 tunani tare da raba su da rayuwar shaye-shaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)