Mu na da kwantan kayayyaki na kimanin tiriliyan 1.4 daga 2024 - MAN

Mu na da kwantan kayayyaki na kimanin tiriliyan 1.4 daga 2024 - MAN

Shugaban ƙungiyar na tarayyar Najeriya, Francis Meshioye ne ya bayyana haka a ranar Laraba, yayin wani taro da ya gudana a jihar Legas.

Meshioye ya ce masana’antun Najeriya sun fuskanci matsalolin tattalin arziƙi da dama da suka kawo tsaiko a  yanayin gudanarwar da ayyukansu a shekarar 2024.

A cewarsa, hauhawar farashin kayayyaki, karyewar darajar Naira, ƙarin kuɗin ruwa da na wutar lantarki, baya ga ƙarin kuɗaɗen haraji da raguwar sayen kayayyaki daga bangaren kwastomomi, na daga cikin abubuwan da masana’antu su ka yi fama dasu a shekarar 2024.

Ya ƙara da cewa waɗannan ƙalubale ne suka sanya aka samu raguwar kuɗaɗen shiga haɗi da raguwar gudunmawarsu a ma’aunin tattalin arziƙi na ƙasar GDP.

Domin magance waɗannan matsaloli, shugaban ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta amince da sabbin kuɗurorin haraji 4, magance hauhawar farashin kayayyaki, baya ga samar da dokar tallata kayayyakin da aka samar a Najeriya, gyara tituna da tashoshin jiragen ƙasa da na ruwa, tare da duba yanayin ƙuɗaɗen wutar lantarki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)