Yayin da ya gurfana a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa saboda zargin yin zagon kasa ga ɓangaren man, Kyari ya ce a matsayinsa na shugaban NNPC tare da kamfanin sun fuskanci kalaman cin zarafi da kuma bata musu suna daga kafofi da dama.
Kyari ya ce NNPC za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta kamar yadda doka ta tanada, yayin da ya yi watsi da masu cin mutuncin su da kuma alkawarin yi wa ƙasa aiki.
Takaddama ta kaure tsakanin kamfanin Dangote da NNPC dangane da rashin ba shi ɗanyan mai da kuma zargin kamfaninsa da gabatar da man da ba shi da inganci, abin da ya kai ga mahawara mai zafi a faɗin Najeriya.
Daga bisani shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bai wa NNPC umarnin sayar wa Dangoten mai a farashin naira.
Najeriya ta bada umarnin sayar wa Ɗangote ɗanyen mai a farashin naira
Gwamnatin Najeriya ta bada umarnin a sayarwa da matatar mai ta Dangote da sauran ƴan ƙasar masu buƙatar ɗanyen mai.
Jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartaswa na gaggawa da gwamnatin ta gudanar, ta kuma bada umarnin sayarwa da masu buƙata ɗanyen mai a kudin Naira a maimakon Dala.
Da yake yiwa manema labarai ƙarin haske, shugaban hukumar tattara haraji na ƙasar Zacch Adedeji ya ce wannan zai sauƙaƙawa masu sayen ɗanyen mai a cikin gida.
Ta cikin wata sanarwa da mai taimakawa shugaban ƙasar kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar, ya ce daga yanzu gwamnati ta soke duk wani cinikin ɗanyen mai a cikin gida da kuɗin dala.
Bayanai na nuna cewa matatar mai ta Dangote kaɗai na buƙatar manyan jiragen ruwa 15 na ɗanyen mai kowacce shekara, inda jimillar kuɗin su ya tasamma dala biliyan 13.5, sai dai kamfanin NNPC ya ce zai iya samar da guda 4 ne kachal.
Majalisar zartaswar a yayin zamanta na yau ta amince da baiwa matatar mai ta Dangote da sauran ƙananan matatu dake cikin gida ganga dubu 450 kowacce rana, kuma za’a riƙa lisaffin nairar ne kan chanjin kuɗin dala na kowacce rana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI