Ministan makamashin Najeriya ya koka kan yadda ƙasar ta kasa cimma burin wadatar lantarki

Ministan makamashin Najeriya ya koka kan yadda ƙasar ta kasa cimma burin wadatar lantarki

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa yawaitar barnar da ake tafkawa a kan muhimman na’urorin samar da hasken wutar lantarki a ƙasar shi ya haifar da cikas wajen cimma burin samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 6,000 nan da Disamba 2024.

Ya bayyana cewa gwamnati ta aiwatar da matakan kaiwa ga gaci kuma tana kan hanya har sai da wasu da dama da suka barna a tasoshin wutar lantarki suka kawo cikas ga shirin.

Mai ba da shawara na musamman kan harkokin sadarwa da hulda da manema labarai, Bolaji Tunji ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta musamman da ya yi da Sunday PUNCH da ake wallafa ta a Najeriya.

A halin yanzu wutar lantarkin Najeriya tana tsakanin megawatt 4,000 da megawatt 4,900 daga tashoshin samar da wutar lantarki guda 19 dake samar da hasken lantarkin ga ƙasar gaba ɗaya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)