Kamfanin Meta da ya mallaki kafafen sada zumuntar Facebook, Instagram da Whatsapp ya bayyana biyan kuɗin a matsayin wani gagarumin ci gaba da ya samu a bangaran biyan waɗanda suka cancanci a ɗora talla kan bayanan da suke wallafawa.
A wani bayani da ya fitar kamfanin Meta ya ce tun a shekarar 2017 ya faɗaɗa hanyoyin da masu amfani da kafofen sada zumuntansa za su samu kuɗin shiga ta hanyar wallafa hotuna da rubutu da bidiyo da kuma gajerun bidiyo da aka fi sani da reels.
“Yayin da muke faɗaɗa hanyoyin da masu amfani da kafafenmu za su samu kuɗin shiga ta hanyar wallafa rubutu da bidiyo masu tsayi da gajerun bidyo da hotuna, kuɗin da muke biyan waɗanda suka cancanci wannan dama ya ƙaru sosai”
“A shekarar da ta gabata (2023) Facebook ya biya masu wallafa rubutu da bidiyo da hotuna da gajerun bidiyo dala miliyan 2. A wanann lokaci gajerun bidiyo na reels da kuma bidiyo mara tsayi sosai sun samu karin kaso 80: a cewar kamfanin Meta
Facebook, TikTok, Twitter, YouTube da Instagram REUTERS - Dado RuvicSabbin bayanan da Meta ya fitar kan hanyar samun kuɗi a Facebook
Wannan sanarwa ta zo lokacin da Facebook ya fito da sabuwar hanyar da masu amfani da shi za su iya samun kuɗi ta hanyar wallafa bidiyon da suka ƙirƙira.
A halin yanzu Facebook ya haɗe kuɗin da yake biya daban-daban zuwa wuri guda, kuma kuɗin da ya haɗe sune na talla da yake sawa a bidiyon da masu amfani da shi suka wallafa da na gajerun bidiyo da aka fi sani da reels da kuma kuɗin da yake biya na rawar da abinda aka wallafa ya taka.
Meta ya ce wannan haɗe kuɗin da ake biya wuri guda zai taimakawa masu amfani da Facebook samun kuɗi da yawa ta hanyoyi daban-daban.
Yadda wasu suka gaza cika ƙa’idar samun wannan kuɗi daga Meta
“Muna farin cikin yadda tsarin biyan kuɗinmu ya taimaki masu wallafa a shafin Facebook, amma mun sani cewar rashin samun dama da wasu suka yi da ka’idojin da muka sanya da hanyoyin da ake bi kafin a samu shiga wasu shirye-shiryenmu, wasu mutane da dama sun rasa wannan dama da ma rasa kuɗin da muke bayarwa”
“Bayanan da muke da su sun tabbatar da cewa kaso 1 bisa 3 na waɗanda suka nemi shiga tsarin biyan kuɗi na shirye-shiryen Facebook ne suka samu wannan dama” a cewar Meta
Google, Amazon, Facebook, Apple da Netflix, REUTERS - Regis DuvignauSaukaka hanyoyin samun kuɗi a Facebook
A yanzu masu amfani da shafin Facebook suna da damar shiga shirye-shirye na samun kuɗi ta hanyar rijista da tsari guda 1, wanda zai tattara duk kuɗin shigar da mutum ya tara daga kowanne shirin.
Wannan sauyi da kamfanin Meta ya samar zai sauƙaƙa hanyoyin samun kuɗin shiga kan duk nau’ikan bayanan da mutum ke wallafawa kama daga rubutu, hotuna, bidiyo da ma gajerun bidiyo.
Meta ya ce zai na biyan masu wallafa bayanai da suka cancanci samun kuɗi a shirye-shiryensa ne daidai da irin yadda aka kalli abinda suka wallafa da kuma nisan wurin da aka kalla da ingancinsa.
“Idan ka samu nasarar shiga tsarin da za muna saka talla a gajerun bidiyo da ka wallafa na reels, to wannan zai ci gaba amma mutum zai iya samun karin kuɗi ta hanyar dogayen bidiyo da hotuna da rubutu idan baka samu damar ba tun a farko”. A cewar Meta
Kamfanin ya ce tuni ya fara aikewa da gayyata ga masu wallafa bayanai mutum miliyan 1 domin su shiga shirin da zai basu gwagwgwabar dama. Kamfanin ya ce yana shirin ci gaba da tura wannan gayyatar a watanni masu zuwa.
Kamfanin Meta ya ce tun daga watan Uli na shekarar 2024 da muke ciki masu amfani da Facebook a kasashen Najeriya da Ghana suka samu damar cin gajiyar wannan shiri na samun kuɗi, kuma wannan ya buɗe damar da ga masu wallafa bayana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI