Majalisar dinkin duniya ta bada tallafin ne ta asusun bada agajin gaggawa. Tallafin zai shafi jihohin Borno, Bauchi da Sokoto saboda irin mummunar illa da ambaliyar ta yi a arewa maso gabashin ƙasar.
Ambaliyar ruwan ta shafi sama da mutum miliyan 1 da dubu 200 a jihohi 31 a Najeriya tare da shafar filayen noma da yawansu yakai hekta 127,500 a ƙasar kamar yadda hukumar bada agajin gaggawa NEMA ta tabbatar.
A cewar babban jami’in majalisar dinkin duniya a Najeriya Mohamed Malick Fall, ambaliyar ruwan ta zama karin ibtila’i kan wanda yankunan ke ciki tare da jefa jama’a cikin wahala.
Wannan tallafi kari ne kan dala miliyan 6 da hukumar jin kai ta Najeriya ta fitar domin taimakawa waɗanda ambaliyar ta shafa.
A shekarar 2022 sama da mutum 500 suka mutu yayin da mutum miliyan 1 da dubu 400 suka rasa muhallansu saboda mummunar ambaliyar ruwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI