MDD ta ce ba a samu nasara ba ko kaɗan a aikin tsaftace yankin Niger Delta

MDD ta ce ba a samu nasara ba ko kaɗan a aikin tsaftace yankin Niger Delta

Shekaru fiye da 40 al’ummar yankin na Niger Delta suka shafe suna fama da matsalar gurɓacewar muhalli, saboda malale gonaki, ƙoramu da sauran muhimman wuraren da ɗanyen man fetur ya daɗe yana yi a yankin mai ɗumbin arziƙin man fetur.

Wannan ce ta sanya Majalisar Ɗinkin Duniya ƙaddamar da bincike kan girman matsalar, abinda ya sanya kamfanonin haƙar mai suka kafa gidauniyar dala biliyan 1 domin aikin tsaftace muhallin da ya gurɓata, a ƙarƙashin jagorancin gwamnatin Najeriya da kuma taimakon jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya.

Sai dai shekaru da dama bayan hakan, bincike ya gano cewar an gaza samun nasara ko da kuwa ‘yar ƙanƙanuwa a dalilin cin hanci da rashawa, da rashin ƙwarewar kamfanonin da aka ɗorawa alhakin tsaftace yankin na Niger Delta, da kuma yaudara ko zamba cikin aminci wajen wallafa rahoton bibiyar yadda aikin ya gudana.

Ga misali cikin shekarar 2021 Majalisar Ɗinkin Duniya ta fallasa cewar an yi kutunkutun wajen tsige sabon shugaban hukumar Hyprep da aka ɗorawa alhakin jagorancin aikin na tsaftace Niger Delta, saboda kokarin da yayi wajen gudanar da bincike kan zarge-zargen badaƙalar kwangilolin da aka yi, wanda aka maye gurbinsa da tsohon shugaban hukumar da aka kora.

Daga ƙarshe dai a cikin shekarar 2023, Majalaisar Ɗinkin Duniya ta janye tallafin aikin da take bai wa hukumar Hyprep din ta Najeriya, saboda dalilai masu alaƙa da matsalar rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)