Hukumomin agajin Majalisar sun ce suna bukatar akalla dala miliyan 148 domin ci gaba da gudanar da aikin agaji a Maiduguri ta hanyoyi daban daban da za su taimakawa mutanen yankin da abincin da za su ci.
Shugaban hukumomin jinkai na Majalisar a Najeriya Mohammed Fall ya gabatar da wadannan alkaluma a daidai lokacin da ake ci gaba da aikin jinkai a birnin.
Kakakin Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya Steffan Dujjaric ya ce wakilan hukumomin jinkai na majalisar tare da na kungiyoyin fararen hula da kuma na kungiyar agaji ta Red Cross sun ziyarci birnin a karshen mako domin tantance bukatun jama'a da kuma gabatar da aikin agajin.
Dujjaric ya ce tawagar ta gana da mutane da dama da iftila'in ta shafa baya ga matsalar boko haram da ta raba wasu daruruwan mutane da gidajen su.
Jami'in ya ce majalisar tare da kawayen su yanzu haka su na gabatar da dafafen abinci da ruwan sha ga jama'a, tare da amfani da jirgin sama wajen kaiwa ga wadanda ke makale a yankunan da ambaliyar bata janye ba.
Majalisar na kuma samar da tsaftacacen ruwan sha ga jama'a domin kaucewa barkewar cutar dake da nasaba da gurbataccen ruwan sha, baya ga taimakawa mata da 'yam mata da kayan tsaftar da suke bukata.
Masu aikin jinkai a Maiduguri REUTERS - Ahmed KingimiEmmanuel Bigenimana, jami'in hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya ya ce bayan shawagin da suka yi da jirgin WFP a kan birnin Maiduguri, hankalinsu ya yi matukar tashi a kan abubuwan da idanunsu suka gani, musamman yadda ambaliyar ta mamaye gidaje da hanyoyi da makarantu da asibitoci tare da gurbata ruwan shan jama'a.
Bigenimana ya ce ya ga mutane tsakanin dubu 200 zuwa dubu 300 sun mamaye sansanonin 'yan gudun hijira saboda babu inda za su tafi, baya ga wasu dubbai da suka tafi gidajen 'yan uwansu a yankunan da matsalar bata yi kamari ba.
Jami'in ya ce yanzu haka jami'an su na dafa abinci a sansanonin 'yan gudun hijira 3 dake suka hada da' Teachers’ Village' da Asheikh da kuma Yerwa domin samarwa akalla kananan yaran da ke zaman gudun hijira dubu 50 da abinci, baya ga iyayen su da suka rasa gidajen su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI