Mayakan Boko Haram sun kashe masuntan Najeriya 14 a Nijar

Mayakan Boko Haram sun kashe masuntan Najeriya 14 a Nijar

Masuntan dai na daga cikin dubban 'yan Najeriya da suka tsere daga gidajensu a arewa maso gabashin kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a Afirka inda suka fake a makwabciyarta Nijar domin gujewa munanan hare-hare daga kungiyoyin masu da'awar jihadi.

Masuntan daga garuruwan Malam Fatori da Doron Baga a Najeriya, mayakan jihadi na Boko Haram ne suka kama tare da kashe su a yankin Bosso da ke yankin Diffa, kusa da kan iyaka da Najeriya, a lokacin da suke kamun kifi. Lamarin dai ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata, sai dai kuma labari ya yi tafiyar hawainiya saboda matsalar sadarwa a wadannan yankuna masu nisa.

“Masunta 14 da ke aiki a yankin Bosso da ke kusa da kan iyaka ‘yan ta’addar Boko Haram suka tsaga maƙogwaronsu,” in ji Babakura Kolo, wani mamba na ƙungiyar masu fafutukar yaƙi da yan Boko Haram da ke taimaka wa sojojin yaƙi da ƙungiyoyin yan ta’adda a arewa maso gabashin ƙasar.

 ‘Yan gudun hijirar da suka dogara da agaji daga kungiyoyin agaji na kasa da kasa, suna yin kamun kifi, saren daji da kuma tsinke karafa domin samun kudin ciyar da kansu. Tafkin Chadi da ya ratsa Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi, ya zama mafakar mayakan Boko Haram da ISWAP, inda suke kai hare-hare a wadannan kasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)