Mayakan boko haram sama da dubu 170 suka aje makamansu - Gwamnatin Borno

Mayakan boko haram sama da dubu 170 suka aje makamansu - Gwamnatin Borno

Kwamishinan yada labarai Farfesa Usman Tar ya bayyana haka  dangane da tashin hankalin da ya yi sanadiyar rasa dubban mutane da kuma raba sama da miliyan 2 da muhallinsu lokacin da ya ziyarci RFI Hausa.

Farfesa Tar yace shirin na su na afuwa da suka yiwa suna 'Borno model for peace, reconciliation and development' ya taimaka wajen haifar da zaman lafiya a sassan jihar.

Kwamishinan ya ce tun shekarar 2021 da Abubakar Shekau ya kashe kansa, gwamnan jihar Farfesa Babagana Zulum ya kira taron jama'ar jihar wanda ya goyi bayan matakan da gwamnati ke dauka na tabbatar da zaman lafiya da kuma aiwatar da shirin afuwar.

Tsohon shugaban Najeriya Umaru Yar'Adua ya fara aiwatar da shirin afuwa a Najeriya ga masu cin amanar kasa wajen  fasa bututun mai a yankin Neja Delta a shekarar 2009 Tsohon shugaban Najeriya Umaru Yar'Adua ya fara aiwatar da shirin afuwa a Najeriya ga masu cin amanar kasa wajen fasa bututun mai a yankin Neja Delta a shekarar 2009 (Photo : Reuters)

Tar ya ce a karkashin shirin an umarci duk wani 'dan bindiga da yake bukatar aje makaminsa da ya kai kansa wurin sojoji wadanda daga bisani zasu tantance shi tare da mikawa jami'an gwamnati wadanda ke aiwatar da shirin sulhun bayan kwance musu damara.

Kwamishinan yace shirin ya samu karbuwa sosai ganin yawan mayakan da suka aje makamansu, aka kuma horar da su wajen sauya musu tunani tare da sanya su cikin jama'a.

Tuni wannan shiri ya samu goyan bayan Majalisar dikin duniya lokacin da Sakatare Janar Antonio Guterres ya ziyarci Maiduguri domin ganewa idansa irin matakan da gwamnatin jihar ke dauka na magance matsalar da ake fuskanta.

Farfesa Tar ya ce a halin yanzu an samu karuwar ayyukan noman da akeyi a jihar wanda yake taimakawa jama'a wajen samun abincin da ake nomawa la'akari da cewar akasarin mutanen jihar manoma ne.

Hukumomin Chadi a lokacin karbar tubabbun mayakan  Boko Haram 46 Hukumomin Chadi a lokacin karbar tubabbun mayakan Boko Haram 46 © MNJTF

Jami'in yace an samu karuwar ayyukan gona sosai a wannan daminar da ta gabata, yayin da kuma yanzu jama's suka rungumi noman rani tare da samun tallafin gwamnatin jihar.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewar babu gaskiya a labarin da wasu ke yi cewar har yanzu a kwai wasu kananan hukumomin dake karkashin ikon boko haram a fadin jihar, saboda jajircewar da sojoji keyi da kuma shirin da gwamnatin jihar ke yi.

Dangane da shirin mayar da mutane garuruwansu kuwa, Farfesa Tar yace aikin ya yi nisa sosai, la'akari da yawan jama'ar da aka mayar garuruwansu bayan sake gina musu gidaje da makarantu da kuma asibitoci, yayin da ya kara da cewa ko a wannan watan a kwai wasu da dama da za'a mayar garuruwan na su.

Kwamishinan ya yi watsi da masu zargin cewar ana tilastawa mutane komawa garuruwan na su ba tare da samun tsaron da ake bukata ba, ya yin da yace bayan sake gina garuruwan sai jami'an tsaro sun tabbatar da zaman lafiyar yankunan kafin a kai mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)