Mayaƙan ISWAP sun kashe sojojin Najeriya 5 a wani hari da suka kai ƙarshen mako

Mayaƙan ISWAP sun kashe sojojin Najeriya 5 a wani hari da suka kai ƙarshen mako

A cewar wasu jami’an sojoji biyu da suka nemi a sakaya sunansu, sun shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, a ranar Asabar ne maharan da suka fito daga ƙungiyar ISWAP sun kai harin sansanin sojin da ke garin Kareto na jihar Borno.

Mun rasa sojojinmu 5 a musayar wuta wasu 10 sun samu rauni, 4 daga cikin jami’anmu kuma sun ɓace muna ci gaba da nemansu.

Haka nan ɗayar majiyar, ta ce ƴan bindigar sun kuma tafi da wasu manyan motocinsu huɗu da ke ɗauke da bindigogin kakkaɓo jiragen sama, tare da kona wasu motoci biyar.

Dama dai a cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta ISWAP ta fitar a jiya Lahadi, da aka wallafa a shafin SITE da ke bibiyar harkokin ƙungiyoyin ƴan ta'adda, ta yi iƙirarin kashe sojoji sama da 20 a wani harin ƙunar baƙin wake da taka kai da wata mota, sannan ta kuma ce ta kona wani sansanin soji da motocinsu 14.

Garin Kareto da ke da nisan kilomita 153 daga birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno, nan ne bataliya ta 149 ta sojojin Najeriya da ke yaki da mayaƙan ISWAP da Boko Haram ta ke.

An kuma ɗauki tsawon lokaci mayaƙan ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi na yunkurin kai wa wurin hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)