Wasu jami’an soji 2 ne suka tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na AFP kisan sojojin 6 na Najeriya a arewa maso gabashin ƙasar.
Mayaƙan ISWAP akan motoci da babura ne suka ƙaddamar da hare-hare a ranar Lahadi a sansanin soji da ke Sabon Gari a Damboa ta jihar Borno.
Mayaƙan sun bankawa sansanin wuta tare da kone ababen hawan soji kamar yadda majiyar sojin da bata yadda a ambaci sunanta ba ta tabbatar.
Sojojin 6 sun rasa rayukansu bayan artabu da ƴan ta’addan da suka kai musu hari, abin da ya tirsasawa sojin janyewa.
To sai dai bayan janyewar sojin ne kuma suka samu ɗauki ta sama inda aka yiwa ƴan ta’addar ruwan wuta babu ƙaƙƙautawa, wanda hakan ya janyo lalacewar motocin soji amma jami’in sojin bai bada adadin ƴan ta’addan da suka mutu ba a gumurzun.
Tun a shekarar 2009 ne yankin arewacin Najeriya ke fama da ayyukan mayakan jihadi da suka haɗa da Boko Haram da ISWAP da sauran masu ɗauke da makamai.
Yaƙin ya haddasa kashe mutum dubu 40 da kuma raba mutum miliyan 2 da muhallansu a arewa maso gabashin Najeriya.
A watan Nuwamba ma sojin Najeriya 5 ne suka rasa rayukansu yayin da 10 suka samu raunuka bayan harin da mayaƙan ISWAP suka kai musu a sansaninsu da ke Kareto kusa da iyakar Jamhuriyar Nijar da Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI