Mayaƙan Boko Haram sun kaddamar da wani sabon hari a jihar Yobe

Mayaƙan Boko Haram sun kaddamar da wani sabon hari a jihar Yobe

Rahotanni sun ce har yanzu babu cikakkun alƙalman mutanen da aka kashe yayin harin, bayan kona gidaje da kuma shagunan al’umma da ƴan ta’addar suka yi.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Dandus Abdulkarim ne ya shaidawa manema labarai batun sabon harin, inda ya ce har yanzu suna kan tattara alƙalman mutanen da aka rasa.

Dangus ya kuma ce harin ya faru da misalin ƙarfe 4 na yammacin jiya, inda mayaƙan suka afkawa ƙauyen da manyan makamai haye kan babura sama da 50 kuma nan take suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Bayanai sun ce bayan ƴan ta’addar sun gama aika-aikar su ne kuma suka fara rabawa jama’a wasu takardu ɗauke da rubutun larabci da ba’a tantance me aka rubuta ba.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa harin na zuwa ne kwana biyu kachal bayan makamancin sa da aka kai makarantar allo a wani ƙaramin ƙauye da ke gab da garin Geidam na jihar Yobe inda nan ma aka kashe guda 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)