Wasu bayanai sun ce yayin ziyarar da ya kai da dakarun rundunar sojin Najeriya a jihar Sokoto muƙaddashin babban hafson sojin Najeriyar laftanal janar Olufemi Oluyede ya umarci dakarun su kakkaɓe barazanar sabuwar ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa.
Ko a ƙarshen mako ƙungiyar ta Lakurawa ta hallaka mutane aƙalla 15 baya ga kwashe tarin dukiyoyi a garin Mera na jihar kebbi, wannan ya sanya ƙungiyoyi da dama tsananta kiraye-kiraye ga mahukuntan Najeriyar don kawar da ƙungiyar tun gabanin ta bunƙasa.
Dangane da wannan wakilinmu Faruk Mohammed Yabo ya yi mana duba kan yadda wannan ƙungiya ta faro da kuma tushenta ga kuma rahoton da ya haɗa mana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI