Saɓanin yadda hauhawar farashin kayaki ya sassuto a watannin Yuli da Agusta, NBS ta ce matakin ƙarin farashin man fetur da mahukuntan Najeriyar suka yi a watan na Satumban ya sake ta’azzara matsalar ta tsadar kayaki.
Masana na kallon halin matsi da tsadar kayakin da al’ummar Najeriya ke fuskanta a yanzu haka ya iya zama mafi ƙololuwa da aka gani a wannan zamanin.
Cikin shekarar nan kaɗai mahukuntan Najeriyar sun ƙara farashin man fetur sau 5 a jare da juna, lamarin da ya sake ta’azzara matsalar ta hauhawar farashin kayaki musamman a ɓangaren da ya shafi kayan masarufi.
Tun gabanin sake hauhawar farashin dama ƙwararru sun yi hasashen cewa tsagaitawar hauhawar farashin ya iya zama na wucin gadi a Najeriyar lura da rashin matakan da za su sauƙaƙa rayuwa.
Bugu da ƙari manufofin kuɗin da ƙasar ke tafiya akai na ci gaba da takure marasa ƙarfi, a wani yanayi da babban bankin Najeriyar CBN ke shirin gabatar da sabon kuɗin ruwan da bankuna za su ci gaba da biya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI