Sanarwar da Olufemi ya fitar ta ce, yau ta zama wata rana da aka samu gagarumin ci gaba a Najeriya, saboda fara aikin matatar Fatakwal mallakin gwamnati, kuma hakan na nuni da cewa an dauƙo hanyar inganta fannin mai da tattalin arziƙin ƙasar.
Soneye ya kuma ce motocin za su fara dakon mai daga yau Talata, inda ya kara da cewa kamfanin NNPCL na aiki ba dare ba rana domin matatar mai ta Warri ta dawo aiki nan bada jimawa ba.
Sanarwar ta kara da taya shugaba Bola Ahmed Tinubu da manyan jami’an gwamnati murna, musamman shugaban NNPC, Mele Kyari, saboda jajircewarsu wajen ganin wannan al’amari ya tabbata.
Fara aikin matatar man fetur ta Fatakwal dai na zuwa ne bayan sanya lokuta mabanbanta da gwamnati ta yi domin fara aikinta, amma sai zuwa wannan lokaci ta soma aikin saboda gyararrakin da aka yi mata.
Idan za’a iya tunawa dai an soma aikin gyara matatar tun a shekarar 2021 lokacin mulkin shugaba Muhammadu Buhari.
Masana a harkar ma’adinai na ganin fara aikin guda daga cikin matatun Najeriya, zai zama mafita ga ƙaranci da hauhawar farashin man fetur da ake samu a ƙasar, yayin da ƴan Najeriyar ke ci gaba da bayyana halin matsin rayuwa da suke ciki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI