Matatar man Dangote ta fara fitar da man fetur na farko ga yan Najeriya

Matatar man Dangote ta fara fitar da man fetur na farko ga yan Najeriya

Kimanin tankokin mai 500 ne a ne kamfanin mai NNPCL ya isar da su  matatar mai da ke da tazarar kilomita 70 a gabashin birnin Legas, babban birnin tattalin arzikin Najeriya, domin daukar lita miliyan 25 na man fetur da ake kira PMS (Premium).

Aliko Dangote ya kasha kimanin dala biliyan 20 kusan Yuro biliyan 18.1, a wannan aiki na matata.

Ana kuma sa ran wannan matata za ta iya biyan dukkan bukatun man fetur na Najeriya ,kasar da ta fi yawan al'umma a Afirka, da kuma fitar da wani bangaren man da ake hakowa zuwa kasashen waje.

Matatar Dangote dake Lagos Matatar Dangote dake Lagos REUTERS - TEMILADE ADELAJA

Najeriya ce kasa mafi arzikin man fetur a Nahiyar Afrika, amma tana shigo da kusan dukkanin bukatunta na man fetur daga waje.

 Kasar tana da matatun mai na jihohi hudu (a Warri, Fatakwal da Kaduna), amma babu wanda yake aiki daga cikin su.

Hukumomin wannan kasa ta bakin Ministan kudi na Wale Edun, wanda ya halarci aikin nay au lahadi, ya yi maraba da jan kokarin yan Najeriya ga baki daya, ya na mai cewa aikin nay au zai bunkasa masana'antu" kasar.

Ana kyautata zaton kusan kashi "44% na man da za a tacewa daga masana’antar Dangote zai biya bukatun Najeriya,banda haka za a shigar da kusan kashi 56% na abin da za a fitar zuwa kasashen waje, wanda hakan zai taimaka don shigo da kudaden waje.

Matatar man Dangote Matatar man Dangote AP - Sunday Alamba

Matatar Dangote da aka sha dage soma aikin ta, an dade ana gabatar da ita ga jama’a domin ganin an shawo kan matsalar karancin man fetur da ake fama da shi a Najeriya, tare da samun saukin farashi a gidajen mai.

 Farashin man fetur da farko ya rubanya sau uku bayan hawan shugaba Bola Ahmed Tinubu kan karagar mulki. Ƙarshen ya kawo karshen tallafi kan mai ,mwanda bai hana yan kasuwa a farkon watan satumba, aiwatar da wani kari na ba-zata da kusan kashi 45% na farashin man a gidajen sayar da man a Najeriya, abin da ya fi wuya 'yan Najeriya su amince da shi, yayin da kasar ke cikin mawuyacin hali na tabarbarewar tattalin arziki, inda hauhawar farashin kayayyaki ya haura kashi 33% a watan Yuli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)