Da safiyar yau Lahadi ne matatar ta Dangote ta bakin jami’in hulda da jama’arta Anthony Chiejina ke sanar da wannan mataki da tuni ya samu maraba daga ƴan kasuwa.
A baya-bayan nan anga yadda farashin man na fetur ya kai ƙololuwa inda a jihar Lagos da ke da saukin farashi ake sayen duk lita guda kan farashin 1080 a wasu wuraren yayinda gidajen man NNPC ke sayarwa akan farashin 1025, lamarin da ya sake tsawwala tsadar rayuwar da jama'a ke fama da ita.
A gefe guda farashin man ya tasamma Naira dubu 1 da 200 a wasu sassa na arewacin ƙasar musamman yankin gabashi da fetur ɗin ya fi tsada.
Zaftare farashin da matatar man ta Dangote ta yi kai tsaye ya na nufin cewa farashin matatar mai zaman kanta ya yi ƙasa da farashin kamfanin mai na gwamnatin ƙasar.
Masana na ganin sassauta farashin daga matatar ta Dangote zai taimaka matuƙa wajen rage hauhawar farashin man a sassan Najeriya, a wani yanayi da hauhawar farashin man ya taka muhimmiyar rawa wajen ta'azzara tsadar kayakin da ake fama da shi a ƙasar ta yammacin Afrika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI