Shugaban kamfanin NNPCL Mele Kyari ne ya tabbatar da haka ga ƴan jarida a wata ziyarar gani da ido da ya kai da tawagarsa matatar a yau litinin.
Kafin fara ziyarar ta gani da ido shugaban kamfanin mai na Najeriya Mele Kyari ya ce za mu ganewa idonmu yadda wannan matata ke aiki dukda ba ta dawo aiki dari bisa dari ba amma ana kan aikin tabbatar da haka.
Matatar ta Warri an ƙaddamar da ita ne a shekarar 1978 kuma kamfanin mai na ƙasa NNPC ke kula da ita kuma za ta na samar da mai a kudancin Najeriya da da kudu maso yamma.
Mutane da dama na ganin wannan abu ba gaskiya bane, suna zaton cewa ba zai yuwu ba a wannan ƙasa don haka muna son ku ganewa idonku zahirin wannan lamari -Kyari
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI