Matatar Dangote zata taimakawa 'yan Najeriya matuka - Kasum Kurfi

Matatar Dangote zata taimakawa 'yan Najeriya matuka - Kasum Kurfi

Wasu 'yan Najeriya sun ce ganin yadda babu wani abinda ya sauya na samun sauki a farashin man da suke saye, ga alama babu wani alherin da za su samu daga wannan sabuwar katafariyar matata.

Sai dai masanin tattalin arziki Dakta Kasum Garba Kurfi ya ce akwai alfanu sosai dangane da wannan matatar da ta fara aiki a Najeriya.

Kurfi wanda ya bayyana haka a cikin shirin Duniyarmu a Yau na RFI Hausa da za'a gabatar a karshen wannan mako, yace irin kayayyakin da matatar Dangote za ta samar ga jama'ar Najeriya su na da matukar yawa wadanda a baya dole sai an je kasashen waje kafin a sayo su.

Masanin ya ce baya ga man dizil da iskar gas na girki da kuma na masana'antu da man jiragen sama, sabuwar matatar za ta samar da sinadarorin robobin da ake amfani da su wajen yin kayayyakin da ake yi da roba da kuma takin zamani da maganin kwari da maganin sauro da man shafawa da wasu ayyuka daban daban.

Kurfi ya kuma ce kusan kashi 70 na ma'aikatan dake aiki a matatar man Dangote 'yan Najeriya ne, wanda hakan ba karamin taimakawa  zai yi wajen rage matsalar rashin ayyukan yi ba da kuma da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Masanin ya ce fara aikin matatar kuma za ta bude kofa ga kasashen duniya da su dinga zuwa Najeriya domin sayen wadannan kayayyaki da kudaden wajen da ake matukar bukatarsu.

Tuni matatar Dangote ta fara sayar da man jiragen sama da kuma dizil a kasashen Turai da kuma Amurka, ya yin da a karshen makon da ya gabata, ta fara sayar da man fetur a cikin gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)