Matatar Dangote ta rage farashin manta da Naira 70.5

Matatar Dangote ta rage farashin manta da Naira 70.5

Wannan na ƙunshe ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rukunin kamfanin Dangote, Anthony Chiejina ya fitar a safiyar yau Alhamis.

Kamfanin ya ce akwai buƙatar ɗaukar wannan mataki saboda sauƙaƙawa al’umma yayin bukukuwa da hutun ƙarshen shekara, baya ga samun sauƙin farashin sufuri da ragin zai haifar.

A ranar 24 ga watan Nuwambar da ya gabata ne dai matatar Dangote da ta zama irinta ta farko a Afrika wadda ba mallakin gwamnati ba, ta rage farashin mai daga N990 zuwa N970, a yanzu kuma ta sanar da sabon farashin na N899.50.

Haka zalika , kamfanin ya fito da wata sabuwar garabasa ga abokan huldarsa, inda a yanzu duk wanda ya biya kuɗin sayen duk lita ta hanyar amfani da takardar kuɗi, to yana da damar sake sayen wata ta hanyar biya da asusun bankinsa.

Idan za’a iya tunawa a ƙarshen makon da ya gabata ne dai ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya IPMAN ta nemi matatar man Dangote da ta yi duba game da rage farashin da ta ke sayarwa ƴan kasuwa daga Naira 970 kan kowace lita, la’akari da cewa farashin dakon mai da ake shigowa da shi daga waje ya ragu zuwa Naira 900.28 a duk lita.

A watan satumbar shekarar 2024 ne dai matatar mai ta Dangote mafi girma a Afirka, mallakin hamshakin attajirin nan na Najeriya, Aliko Dangote, ta fara fitar da man fetur na farko a Najeriya, bayan shafe tsawon shekaru takwas ana aikinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)