
A ƙarkashin wannan sabon tsarin, mazauna birnin Lagos za su rika sayen litar man a kan Naira 860 a gidajen mai na MRS.
Matatar ta Ɗangote ta ce ta ɗauki matakin ƙarya farashin ne domin sauƙaƙa wa ƴan Najeriya gudanar da rayuwarsu a daidai lokacin da suke shirye-shiryen fara azumin Ramadan.
Kodayake za a rika sayar da litar man a kan Naira 870 a sauran jihohin kudu maso yammacin Najeriya saɓanin jihar Lagos, inda farashin ya fi sauƙi da Naira 10.
A can arewacin Najeriya kuwa, za a rika sayar da litar a kan Naira 880. Sai kuma yankin kudu maso kudanci da kudu maso gabashin ƙasar da za su rika sayen litar a kan Naira 890 kamar yadda sanarwar matatar ta fayyace.
Har ila yau matatar ta ce, ɗaukar matakin na da nasaba da nuna goyon baya ga manufofin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu na farfaɗo tare da bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya don rage wa talakawa raɗaɗin da suke fuskanta.
Ba a karon farko kenan ba da Matatar Mai ta Ɗangote ke rage farashin na litar man fetur, domin ko a farko-farkon wannan wata na Fabairu, sai da matatar ta zabtare Naira 60 daga farashin.
Kazalika, ko a cikin watan Disamban bara, sai da Ɗangote ya rage farashin litar da Naira 70.50 a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan ƙarshen shekara, inda mutane suka rika sayen man a kan Naira 899 daga Naira 970.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI