Bayan wani taro da ta gudanar, wanda ya yi nazari a kan irin manufofi da matakan da gwamnatin ke ɗauka, ƙungiyar ta ce rayuwar talakawan Najeriya ya da ɗa tabarbarewa musamman mazauna yankin arewacin ƙasar da ke fuskantar ƙalubale daban daban.
Sanarwar da mai magana da yawun ƙungiyar Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya rabawa manema labarai, ta ce mazauna yankin arewacin ƙasar na fama da tsananin rashin abinci da tsaro da ƙarancin samun damar ilimi da koyan sana’o’i da kuma harkokin kasuwancin da za su dogara da kansu.
Muhammad-Baba ya ce rayuwar akasarin mutanen arewacin ƙasar ya dogara ne ga ƙananan sana’oi, amma yanayin da ake ciki ya jefa da dama daga cikin su cikin halin ƙaƙanikayi da kuma rashin madogara, sakamakon manufofin tattalin arzikin da wannan gwamnatin ke ɗauka a matakin tarayya, ba tare da la’akari da irin uƙubar da yake jefa jama’a ba.
Ƙungiyar ta ce duk da yake ɗaukar irin waɗannan matakai na da matukar tasiri, amma kuma bai da ce ya yi illa ga mutanen da ake cewa ana yi domin su ba, saboda yanayin da ake ciki na iya hallaka wasu daga cikin su ta hanyar da ba za su iya cin moriyar gajiyar da za’a samu ba.
Muhammad-Baba ya ce sun buƙaci shugaban ƙasar da ya sake nazarin takunsa ta hanyar da zai dinga la’akari da rayuwar jama’a, tare da kuma sauraron ƙorafin jama’a domin gyara ga matakan da suke ɗauka waɗanda ke yiwa ƴan ƙasa illa.
ACF ta buƙaci ɗaukar matakan gaggawa ta hanyar aiwatar da manufofin kar-ta-kwana da kuma na dogon zango ta hanyar da za’a samarwa jama’a abinci, ciki hara da shigo da shi daga ƙasashen ƙetare, domin ragewa jama’a raɗaɗin halin da suke ciki.
Ƙungiyar wadda ta ce ta fahimci ƴan arewa ne kawai za su kare martabar yankin, ta buƙaci samun daidaito wajen raba mukamai da kuma gaggauta samo maslaha dangane da matsalar samar da wutar lantarki da talaucin da ya addabi jama’a da rashin ayyukan yi da kuma koma bayan da yankin ke fuskanta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI