Mai magana da yawun rundunar Laftanar kanar Olaniyi Osoba ya bayyana mika wuyar lokacin da yake ganawa da manema labarai a birnin Maiduguri.
Kanar Osoba ya bayyana mika wuyar wadannan fitattun kwamandodi a matsayin gagarumar nasarar da suke sa mu wajen yaki da ayyukan ta'addanci a yankin.
Kakakin yace Keremi wanda na hannun daman shugaban boko haram ne, ya amsa wasu laifuffukan da aka zarge shi da aikatawa na kai hare hare da dama a kan hanyar Monguno zuwa Baga.
Daya daga cikin wadanda suka aje makamansu mai suna Babagana Modu ya bayyana sauya matsayinsa a kan matakan da kungiyar ke dauka a kan jama'a.
Modu ya mika kansa ne tare da wasu mata guda 2 da maza 4 da kuma wasu yara 2.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI