A wani taron manema labarai da ta gudanar, kantomar ta Wudil ta ce an sace injinan saka da aka yi odar su daga waje guda 50 tare da sace buhunan takin zamanin sama da dubu biyu
Ta ce bata-garin waɗanda ta yi ikirarin hayar su aka yi, sun lalata gabakiyan sakatariyar ta Wudil ciki har da ofishinta, inda ta ce gabakiɗayan muhimman takardun an kona su ciki har da takardun jarabawar yara.
Kazalika kantomar ta Wudil ta ce bata-garin sun kuma afka wa kasuwar Kayan abinci ta Darki da ke yankin, inda suka balle shaguna da maajiyar abinci.
Ta ce jami'an tsaro na kan aikin kwato kayayykin da aka sata tare da kokarin gano waɗanda suka ɗauki nauyin matasan.
A yanzu haka kantomar ta Wudil ta koma gudanar da aikinta daga harabar Gidan Radiyon Kano.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI