Masu ɗaga tutar Rasha sun ci amanar Najeriya - Janar Musa

Masu ɗaga tutar Rasha sun ci amanar Najeriya - Janar Musa

Janar Musa na magana ne jim kaɗan da kammala wata ganawa da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi da manyan jami'an tsaron ƙasar a fadarsa ta Aso Rock a daidai lokacin da dimbin matasa ke ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna ɓacin rai kan tsadar rayuwa.

A cewar babban hafsan tsaron, doka za ta yi aiki a kan duk wanda aka samu da aikata wannan laifin na ɗaga tutar Rasha a yayin gudanar da zanga-zangar.

Kazalika Janar Musa ya gargaɗi waɗanda ke kiraye-kiyaren juyin mulki a ƙasar, yana mai cewa, rundunar soji ta amince da tsarin dimokuradiyya, a don haka babu yadda za a yi sake a samu sauyin gwamnati.

Ita ma gwamnatin Rasha ta nesanta kanta daga wannan mataki na ɗaga tutarta a yayin zanga-zangar, tana mai jaddada cewa, ko kaɗan ba ta da hannu a cikin abin da ke wakana yanzu haka a faɗin Najeriya.

An kama tela da wasu 30 kan zanga-zanga da tutocin Rasha a Kano

Ƴan sanda sun tsare wani tela da wasu muane 30 a Kano kan mallaka da kuma daga tutocin kasar Rasha a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa.

Hedikwatar ’yan sandan Najeriya na zargin telan da dinka dimbin tutocin kasar Rasha da masu zanga-zanga ke amfani da su a Kano da wasu Jihohin Arewa.

Har ila yau, an kama masu zanga-zangar akalla 30 da ke dauke da tutocin, saboda hakan laifin cin amanar kasa ne.

Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya shirya.

Wasu masu zanga-zangar adawa da mummunan shugabanci a Arewacin Najeriya sun yi ta daga tutar kasar Rasha suna kira gare ta da ta kawo musu dauki.

A karshen makon ne kuma hotunan masu zanga-zangar dauke da tutar Rasha suka yi fara yawo a kafofin sada zumunta.

Hakazalika an ga bidiyon wasu teloli a cikin shago suna dinka tutocin na Rasha, wanda a jikin bidiyon aka rubuta “Gobe babu.”

Washegari, ranar Lahadin Shugaba Tinubu, a jawabinsa ga al’ummar kasar ya gargadi masu zanga-zangar da su guji bari a yi amfani da su wajen cimma wata manufa da ka iya kawo cikas ga cigaban dimokradiyyar Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)