Ko da ya ke jam’iyyu 18 ne ke fafatawa a wannan zaɓe, guda 3 ne ke sahun gaba, wato PDP mai mulkin jihar, sai APC da Labour.
A karon farko tun bayan shekaar 1999, zaɓen shugaban ƙasa Najeriya ya kasance tsere a tsakanin manyan jam’iyyu 3 a shekarar 2023, wato jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar, sai PDP da APC. Haka zalika a wannan zaɓe na gwamnan Edo, wanda ya saba kasancewa tsakanin manyan jam’iyyu biyu, yanzu ya zama gasa tsakanin manyan jam’iyyu 3 a wannan shekarar.
A jihar Edo, jam’iyyar Labour ta tsohon ɗan takaran shugaban ƙasa, Peter Obi ta shiga gaban dukkanin jam’iyyu 3 da ke kan gaba, wato PDP ta Atiku Abubakar da APC ta Bola Ahmed Tinubu, duk da cewa dukkannin ƴan takarar gwamnan na da ɗimbim mabiya.
A wannan Asabar, 21 ga Satumba, Asue Ighodalo na jam’iyyar PDP; Monday Okpebholo na APC da Olumide Akpata na jam’iyyar Labour za su raba rana, a zaɓen da masu lura da al’amura ke cewa za ayi gogayya mai zafi.
Musayar munanan kalama da tarzoma da ta tashi a wasu sassan jihar a yayin yaƙin neman zaɓe sun sanya fargaba a zukatan al’ummar jihar a yayin da ake tunkarar wannan zaɓe.
Kallo dai ya koma kan jami’an hukumar zaɓe ta Najeriya, inda ake fatan su tabbatar da an gudanr da sahihin zaɓe domin kauce wa tashin hankali, duba da yadda dukannin bangarori na masu ruwa da tsaki a zaɓen ke zargin juna da shirin tafka maguɗi. By Saturday September 21, 2024, Asue Ighodalo of the PDP; Monday Okpebholo of the APC and Olumide Akpata of the LP would slug it out in what is expected to be a keenly contested poll.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI