Masarautar Bauchi ta warware nadin Sanata Buba saboda kalubalantar gwamna

Masarautar Bauchi ta warware nadin Sanata Buba saboda kalubalantar gwamna

 

Sanatan, ya kalubalanci gwamnan jihar ta Bauchi Bala Muhammed kan sukar manufofin shugaban Nigeria Bola Ahmed Tinubu da ya yi.

Wakilinmu a Bauchi Ibrahim Malamgoje ya ce sanarwar kwace matsayin sarautar na kunshe ne cikin wasikar da masarautar ta aike wa Sanatan mai dauke da sa-hannun Nasiru Musa.

Wasikar, ta yi bayanin cewa an dauki wannan mataki ne bayan wani taro da majalisar masarautar ta yi karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu, inda suka tattauna kan kalaman rashin girmamawa da Sanatan ya yi kan gwamnan na jihar Bauchi, inda kuma a karshe majalisar ta amince da kwace matsayin sarautar tasa.

Sanata Shehu Buba Sanata Shehu Buba © Blueprint

Majalisar musamman ma, ta zargi Sanatan da “cin zarafi tare da nuna rashin girmamawa ga Gwamnan Jihar Bauchi”, lamarin da ta ce ya saba da tanade tanaden tsarin al’adun masarautar.

Idan za a iya tunawa yayin kaddamar da yakin neman zaben shugabancin kananan hukumomi na jam’iyyar APC  a jihar Bauchi, Sanata Shehu Buba ya zargi gwamnan Bauchi da karkatar da kayan tallafin da suka hada da shinkafa, masara da takin zamani da gwamnatin tarayya ta tura wa jihar.

Wannan shi ne karo na hudu da masarautar Bauchi ke kwace sarauta saboda matsalar da gwamnan jihar ke samu da wasu. Lamarin ya faro ne da tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara wanda aka kwace sarautarsa ta Jakadan Bauchi, sai Alhaji Muhammad Bello Kirfi wanda aka karbe tasa sarautar ta Wazirin Bauchi da kuma tsohon dan majalisar wakilai Yakubu Shehu Abdullahi wanda aka karbe sarautarsa ta Wakilin Birni sai kuma yanzu da aka karbe sarautar Mujaddadin Bauchi daga Sanata Shehu Buba Umar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)