Wannan ya biyo bayan matsayin Bankin duniya cewar duk da shekarun da aka kwashe a Najeriya da wasu kasashe masu tasowa ana aiwatar da manufofin su, bankin na cewa za'a kwashe shekaru 100 masu zuwa kafin kawar da talaucin da jama'a kusan miliyan 700 ke fama da shi.
Farfesa Muntaqa Usman, masanin tattalin arziki a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria ya ce irin wadannan shawarwarin da hukumomi irin su Bakin duniya da Hukumar bada lamuni ta duniyar, IMF suka bai wa kasashen dake kudancin Amurka sun taimaka wajen durkusar da su sabanin Brazil wadda ta yi gaban kanta wajen samarwa jama'ar ta mafita.
Farfesa Usman ya ce su wadannan hukumomi ne na 'yan kasuwa dake bukatar riba, kuma duk shawarwarin da za su bai wa kasashe masu tasowa na mayar da hankali ne a kan bukatun su, sabanin bukatun kasashen da abin ya shafa.
Shehun malamin ya ce wadannan hukumomin ne suka jefa kasashen dake kudancin Amurka cikin ukubar talauci, kamar yadda kasashen dake kudu da sahara na Afirka wadanda shugabannin su suka yi imani da shawarar dake fitowa daga wurinsu suka shiga.
Usman ya ce abin takaici ne yadda shugabannin kasashe masu tasowa irin su Najeriya ba sa dogara da masanan da suka fito daga kasashensu duk kuwa da tasiri da kuma ficen da suka yi a kasashen duniya, sai dai rugawa zuwa irin wadancan hukumomi dan jin abinda suke so a fada musu.
Dangane da neman mafita kuwa, sai Farfesan ya ce dole 'yan kasa su tashi tsaye wajen ganin shugabannin da suka zaba na aiwatar da manufofin da suka dace da jama'a, musamman abinda ya shafi tattalin arzikin su da kuma rayuwarsu ta yau da kullum, tare da daukar mataki lokacin zabe a kan duk wani shugaban da ya bijire musu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI