Manyan dillalan man Najeriya sun bukaci kotu tayi watsi da bukatar Dangote

Manyan dillalan man Najeriya sun bukaci kotu tayi watsi da bukatar Dangote

Wannan ya biyo bayan karar da Dangote ya shigar inda ya bukaci hana shigo da man domin saye daga wurinsa da kuma bukatar biyansa diyyar naira biliyan 100 saboda lasisin da aka riga aka bayar. 

Dillalan sun ce matakin na Dangote wani yunkuri ne na mamaye harkar man inda shi kadai zai dinga samar da shi da rarraba shi da kuma sanya farashinsa. 

Wadannan dillalai sun ce wannan mataki na Dangoten zai dada jefa tattalin arzikin Najeriya cikin mawuyacin hali da kuma jefa jama'ar kasar cikin halin kakanikayi idan aka bai wa Dangote damar cin karensa babu babbaka a harkar man.

Dillalan sun ce muddin Najeriya ta amince wajen mika ragamar tafiyar da harkokin man dungurungun zai haifar da gagarumar matsala ga harkokin man Najeriya baki daya.

Matatar Dangote Matatar Dangote REUTERS - Marvellous Durowaiye

Dillalan sun ce muddin kotu ta amince da hana NNPC bada lasisin sayo man daga kasashen ketare kamar yadda dokar PIB ta bangaren man ta tanada, Najeriya za ta fada cikin mummunar yanayi karancin man domin kuwa basu da man da zai iya wuce kwanaki 30 ana amfani da shi a rumbunan ajiyarsu. 

Shi dai kamfanin Dangote na cewa bada lasisin shigo da man ya sabawa dokar kasa tunda kamfaninsa na samar da shi a cikin gida, saboda haka yake neman kotu ta haramta daukar matakin.

Alkalin kotun ya sanya ranar 20 ga watan janairun shekara mai zuwa domin sake zama a kan shari'ar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)