Makaman Libya ne ke ta'azzara mana matsalar tsaro - Najeriya

Makaman Libya ne ke ta'azzara mana matsalar tsaro - Najeriya

Shugabar Hukumar Hafsat Abubakar Bakari, ta bayyana hakan lokacin da ta jagoranci wata tawaga a wani taro da Cibiyar Kula da Kamfanoni masu zaman kansu ta kasa da kasa ta shirya a birnin Washington D.C na ƙasar Amurka.

Cikin wata sanarwa da jamui’in hulda da jama’a na hukumar Sani Tukur ya fitar, an ruwaito Bakari na danganta ta’azzara matsalolin tsaron cikin gida a Najeriya da kwarar makamai daga ƙasar Libya.

Hajiya Hafsat wanda ta ce Najeriya ba ta bukatar matakan wucin gadi a yakin ta take yi  da ta’addanci, ta yi kira da a dauki matakai masu dorewa.

Ta jaddada bukatar ƙara azama a dabarun yaki da halasta ƙudaden haramun da Najeriya ke yi, wajen cimma muradun kawo karshen ayyukan ta'addanci a yankin Sahel, ta hanyar shigar da kamfanoni masu zaman kansu domin kaiwa ga gaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)