Makaman da ke hannun ƴan ta'adda mallakin gwamnati ne - Nuhu Ribaɗu

Makaman da ke hannun ƴan ta'adda mallakin gwamnati ne - Nuhu Ribaɗu

Ribaɗu na magane a birnin Abuja a wurin taron lalata makamai da Cibiyar Daƙile Yaɗuwar Ƙananan Makamai ta Ƙasa ta shirya.

A cewar Ribaɗu, waɗannan makaman sun faɗa hannun ɓata-gari ne saboda wasu gurɓatattun jami'an tsaron Najeriya.

Kodayake ya ce, ƙasar na da ikon tunkarar lamurran tsaronta.

Za mu lalubo hanyar kawo ƙarshen wannan lamari. Dole ne mu farfaɗo da ƙasarmu domin rayuwa cikin zaman lafiya

Ribaɗu ya bayyana cewa, mafi munin ɓata-garin shi ne jami'in ƴan sanda ko soja da ke ɗaukar makamai yana sayar da su ko ɓoye su ga miyagun da ke kashe masa abokan aiki.

Dole ne mu yaƙi waɗannan mutanen, kodayake akwai wasu ɓata-garin daga wasu wuraren. Yaɗuwar haramtattun ƙananan makamai na ci gaba da zama babbar barazana ga tsaron ƙasarmu, lamarin da ke tsananta ta'addanci da ayyukan ƴan bindiga da sauran miyagun laifuka. Inji Ribaɗu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)