Kudirin dokar wanda ‘yan majalisu 34 suka gabatar da shi, ya bukaci da a gudanar da zabukan gwamnoni da na shugaban kasa a rana guda.
Kudirin an sake gabatar da shine domin shiga karatu na biyu, wanda dan majalisar Imo Ugochinyere, ya gabatar a zauren majalisar.
Lokacin da shugaban majalisar, Abbas Tajuddeen ya gabatar da sunan kudirin, 'yan majalisar sun yi ta ihun "bama so."
Daga bisani shugaban majalisar ya bayyana cewa, an yi watsi da wannan kudiri da ya gaza samun goyon mafiya rinjaye na 'yan majalisar, awnda ya tsallake karatu na farko.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI