Matakin dai ya biyo bayan gyare-gyaren ƙudirin da gwamnatin tarayya ta yi na ganin an shawo kan matsalar ambaliyar ruwa ga mazauna Borno da kewaye.
A zaman Majalisar ranar Laraba, Amos Magaji, wakilin mazabar Jaba/Zangon Kataf na tarayya, ya gabatar da wani ƙudiri mai matukar muhimmanci ga al’umma, inda ya bayyana irin barnar da ambaliyar ruwa ta yi wa gidaje da kasuwanni da cibiyoyin kiwon lafiya da dama.
Ƙudirin Inuwa Garba
Yayin da Inuwa Garba, Wakilin Mazabar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, ya gabatar da ƙudirin neman tallafin Naira Biliyan 300 don tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa da kuma rage radadin da al’umma suka shiga.
“Duk da cewa daidaikun mutane na bada gudunmawa, wanda abin yabawa ne, ya kamata gwamnatin tarayya kuma ta ware tallafi na musamman na kusan Naira biliyan 300 domin taimawa wadanda lamarin ya shafa a Borno,”
Ƙin amincewa da ƙudirin
Sai dai a lokacin da kakakin majalisar Tajudeen Abbas ya bukaci a kada kuri'a kan gyaran, daga karshe 'yan majalisar suka kada kuri'ar kin amincewa.
A maimakon haka, majalisar ta karfafawa gwamnatin tarayya gwiwa da ta taimaka wa wadanda abin ya shafa gwargwadon iko, ba tare da tantance adadin kudi ba.
Abin da suka amince
Haka kuma ta bukaci ma’aikatar lafiya ta tarayya da ta shiga tsakani domin dakile barnar da ambaliyar ruwa ta yi a asibitin koyarwa na Maiduguri da sauran cibiyoyin kiwon lafiya a jihar.
Majalisar ta bukaci ma’aikatar wutar lantarki ta tarayya da ta gaggauta maido da wutar lantarki a asibitin tare da daukar karin matakan dakile illar bala’in.
‘Yan majalisar dai sun bukaci gwamnatin tarayya da ta fadada taimako zuwa ma’aikatan gidan gyaran hali na Najeriya wadanda ambaliyar ruwan ta shafa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI