Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazak ya shaida hakan ga manema labarai ranar Talata jim ƙadan bayan ganawa daban-daban da bangarorin biyu suka yi da shugaba Tinubu, ƴan kwanaki bayan zanga-zangar ƙin jinin gwamnati da aka yi a faɗin kasar.
Majalisar da ta ƙunshi tsofaffin shugabannin ƙasar zaɓaɓɓu da na mulkin soja, da gwamnoni, da ministoci, da shugabannin majalisar tarayya, sun gana da shugaban ƙasar, kafin daga bisa ƙungiyar gwamnoni ita ta yi nata ganawar, inda suke tattauna halin da ƙasa ke ciki da kuma matakan da ya kamata a ɗauka.
Obasanjo bai halarci taron ba
Cikin tsofaffin shugabannin da suka halarci zaman harda Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan da Abdulsalami Abubakar da Yakubu Gowon sai dai ba’a Olusegun Obasanjo ba.
Taron Majalisar Ƙoli ta Najeriya da shugaba Tinubu Ahmed ya jagoranta. 13/08/24 © Nigeria presidencyMajalisar kan yi zama ne a duk lokacin da wani muhimmin batu ya taso a ƙasar domin bayar da shawarar yadda za a magance shi, kuma wannan ne karon farko da Shugaba Tinubu ke jagorantar taron tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI