Hakanan Majalisar ta kuma umurci kwamitocin tsaro da na hukumar ta kwastam da su binciki irin rawar da jami’an sojin ƙasar da ke taimakawa jami’an kwastam a ayyukan da suke gudanarwa, tare da tabbatar da ganin ayyukansu na gudana akan doka da ka’idojin kare hakkin dan Adama.
Da yake gabatar da kudirin nasa, ɗan majalisar wakilan Wingan ya ce bisa ga sashe na 4 cikin sashi na (b, e, da f) na dokar hukumar kwastam ta Najeriya, ta shekarar 2023, ta ratayawa hukumar ta kwastam umarnin tara kudaden shiga, hana fasa-kwauri da tabbatar da tsaron iyakokin Najeriya.
Sai dai dan majalisar ya yi zargin cewa maimakon hana fasa-kwauri, rahotannin baya-bayan nan sun nuna cewa jami’an hukumar ta kwastam ta Najeriya da ke kan iyakokin kasar na taimakawa wajen gudanar da wasu safara-safara da suka saɓawa dokar da ta kafa hukumar.
Ya sanar da majalisar cewa rahoton da kafar yaɗa labaru ta Sahara Reporters ta fitar a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2024, ya fallasa abin da ya kira safarar motoci sama da 2,000 dauke da shinkafa kilogiram 6,500,000 ta hanyar Badagry, bisa zargin cewa da sanin jami’an Kwastam dake sanya idon a wannan kan iyakar.
Ya kuma ce faifan bidiyo da wani dan jarida mai bincike, Fisayo Soyombo ya wallafa, ya bayar da shaidar hadin kai da jami’an Kwastam ke yi a wadannan haramtattun ayyuka.
Wingan ya ce baya ga zargin taimakawa masu harkar fasa kwauri, an kuma kai rahoton jami’an hukumar ta kwastam kan laifukan cin zarafi da ake yi wa ‘yan kasar da suka yi kokarin tara bayanai da fallasa abubuwan da suka sabawa doka.
Ya kuma ƙara da cewa an samu wasu rahotannin cin zarafi, ciki har da wani lamari da ya faru a kan hanyar Badagry-Seme a ranar 1 ga watan Disambar shekarar 2024, inda jami’an hukumar kwastam tare da hadin gwiwar sojoji suka ci zarafin wasu masu safara guda biyu Taofeek Olatunbosun da Rafiu Abdelmalik.
Ɗan majalisar ya ci gaba da cewa fasa-kwauri na haifar da illa ga tattalin arziki da suka hada da durkusar da masana’antu na cikin gida, da rage kudaden shiga da gwamnati ke samu, da inganta harkokin kasuwanci na rashin adalci, da kuma cika kasuwanni da kayayyakin da ba su da inganci da kuma illa.
Wingan ya ce abin da wasu jami’an hukumar ta Kwastam ke yi ya saba wa aikin da aka dora mata, yana rage mutuncin hukumar a wurin jama’a da kuma sanya shakku kan yadda ake sa ido kan ayyukan tsaro na hadin gwiwa da ya shafi jami’an soji.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI