Majalisar dattawan Najeriya ta kafa kwamitin da zai yi nazari kan dokar haraji

Majalisar dattawan Najeriya ta kafa kwamitin da zai yi nazari kan dokar haraji

Kwamitin zai duba batutuwan da ake cece-kuce a kansu sannan kuma ya dawo domin gabatar da rahotonsa gaban zauran majalisar dattawan ƙasar.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Barau Jibril ne ya sanar da wannan mataki a yayin zaman majalisar na yau Laraba.

Sanata Barau wanda ya jagoranci zaman majalisar na yau, ya ce an samu cece-kuce kan ƙudirin don haka an ɗorawa kwamitin alhakin tattaunawa da ministan shari’a da kuma bangaran zartarwa da kuma sauran masu ruwa da tsaki kan ƙudirin.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ne ya gabatar da kudirori 4 a wata wasika da ya aike a ranar 3 ga watan Oktoba, wanda shugaban majalisar dattawan ƙasar Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai Tajuddin Abbas suka karanta a zaman majalisun biyu.

Tinubu ya ce gyaran dokar zai ƙarfafa harajin da hukumomin ƙasar ke samu, kuma yana cikin kudirin gwamnatin na kawo ci gaba a ƙasar.

To sai dai ƴan Najeriya da gwamnoni da sarakunan gargajiya da kungiyoyi masu zaman kansu da wasu daga cikin yan majalisu a ƙasar sun ƙalubalanci wannan kudiri.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Titus Zam daga Benue da Orji Uzor Kalu na jihar Abia da Sani Musa daga Niger da Abdullahi Yahaha daga Kebbi da sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)