Hakanan Majalisar ta kafa kwamiti mai mambobi takwas, karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, domin gudanar da bincike kan rushe-rushen tun daga lokacin da Wike ya kasance mistan birnin na Abuja.
yunurin ya biyo bayan kudirin da Ireti Kingibe ta gabatar ne a yayin zaman majalisar.
Misis Kingibe, yayin da take gabatar da kudirin, ta ce rusa gine-gine tun farkon jagorancin ministan yaci karo da hukuncin kotu ba.
Sanatan ta kuma ci gaba da cewa rusau da yak e yi ya kara ta’azzara wahala a tsakanin mazauna birnin saboda an mayar da mutane cikin mawuyacin hali.
Sannan Malama Kingibe ta bukaci Sanatocin da su tilastawa Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) da ta dakatar da kwace kadarorin al’uma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI