Majalisar dattawa ta bukaci Tinubu ya kori Danladi Umar shugaban CCT

An dauki wannan kudiri ne bisa tanadin sashe na 157 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya nuna cewa kashi ⅔ ' na yan majalisar dattawa na iya baiwa shugaban kasa shawara kan ya tsige shugaban kotun da’ar ma’aikata (CCT).

Shugaban Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ne ya dauki nauyin kudirin neman a tsige shugaban kotun da’ar ma’aikata (CCT)daga mukaminsa,inda Bamidele, mai wakiltar mazabar Ekiti ta tsakiya, ya ce majalisar dattijai ta samu korafe-korafe da dama da kuma zarge-zargen cin hanci da rashawa da kuma rashin da’a a kan Umar.

Wasu ƴan Najeriya a gaban ɗaya daga cikin bankunan ƙasar. Wasu ƴan Najeriya a gaban ɗaya daga cikin bankunan ƙasar. AP - Dan Ikpoyi

Ya ce ‘yan majalisar sun gayyaci Danladi Umar domin yi masa tambayoyi amma ya ki bayyana. Don haka ya bukaci majalisar dattawa da ta yi amfani da ikonta na tsarin mulki kamar yadda sashe na 157 (1) ya tanada na tsige shi daga mukamin.

Bayan gabatar da jawabinsa, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya gabatar da kudirin a kada kuri’a, sannan Sanatoci 84 da suka hallara a zauren majalisar suka kada kuri’ar amincewa. Bayan kidaya kuri’un, Akpabio ya sanar da kudurin majalisar dattijai na neman a tsige Danladi Umar.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu © Nigeria Presidency

Za a mika kudurin ne ga shugaban kasa Bola Tinubu wanda zai yanke hukunci na karshe kan lamarin. Sai dai ana sa ran shugaban kasar zai mutunta kudurin majalisar dattawa saboda akwai yiwuwar shugabancin majalisar ya tattauna batun da tawagar shugaban kasar gabanin zaman taron na ranar Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)