Dan majalisar ya bayyana cewa, makasudin ziyarar tasa ita ce duba da idon basira irin barnar da aka yi wa kayan aiki da ababen more rayuwa a asibitin sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a Maiduguri da kuma sanin yadda majalisar za ta sa baki domin farfado da cibiyar lafiya a wannan yanki.
Dan majalisar y ace,da zaran ya koma Abuja za su gabatar da kudirin neman agajin gaggawa ga wannan asibitin. Don haka ba wai wani ne ke kawo mana rahoton irin barnar da aka yi ba, mun ga irin abinda ya faru da kuma yadda asibitin ya ke. Da abin da na gani, lallai wannan asibitin yana bukatar kulawar gaggawa.”
Sufurin Kwale-Kwale a Maiduguri REUTERS - Ahmed KingimiDan majalisar ya ce asibiti wuri ne da marar sa lafiya da dama ke zuwa ,da kuma ke bukatar kulawa da ta dace, kuma da zarar an samu bala’i a asibitin, abin ya shafi kowa. Mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar 10 ga watan Satumba, ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 30 tare da jikkata wasu fiye da miliyan daya, a cewar hukumomi. Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne sakamakon rugujewar madatsar ruwan Alau da ke gabar kogin Ngadda a jihar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI