Majalisar Adamawa ta rage ƙarfin ikon Lamido Barkindo

Majalisar Adamawa ta rage ƙarfin ikon Lamido Barkindo

A ranar Litinin ne Gwamna Fintiri ya mika wa majalisar bukatar amincewa da dokar nada sarakunan jihar Adamawa, Kudurin dokar ya baiwa gwamna ikon kafa masarautu da nada sarakuna ko kuma tsige sarakunan gargajiya.

Rahotanni sun ce cikin kwanaki biyu kachal majalisar ta gabatar da kudirin ta yi mahawara da kuma amincewa da dokar wanda yanzu haka take gaban gwamna Ahmadu Fintiri domin rattaba mata hannu.

Abin da Sabuwar dokar ta ƙunsa

Sabuwar dokar ta tsige Lamidon Adamawa Mustapha Barkindo a matsayin shugaban majalisar sakarakunan jihar Adamawa na dindindin, a madadin haka, shugabancin zai zama na ƙarba ƙarba ko wace shekara a tsakanin dukkan sarakuna da masu daraja ta daya.

‘Yan majalisar sun bayyana cewa tsarin karba-karba na da nufin tabbatar da adalci, daidaito da kuma daidaiton wakilci a shugabancin gargajiya.

Gwamna Fintiri, wanda tun farko ya amince da dokar samar da gundumomi a yayin wani biki na sirri a gidan gwamnati, ya bayyana cewa an tsara dokar ne domin inganta harkokin mulki da magance matsalolin tsaro.

Rage darajar sarki Barkindo

Sabon tsarin ya rage tasirin da ƙarfin ikon Lamido sosai, daga ƙananan hukumomi 8 zuwa 3 kacal. Kafin ita wannan dokar kananan hukumomin Hong da Song da Gombi da Fufore da Girei da Yola ta Arewa da Yola ta kudu da kuma Mayo Belwa suna karkashin Lamidon ne, amma yanzu ikon sa zai tsaya a ƙananan hukumomin Girei da Jimeta da kuma Yola. Wannan dokar ta shafi ikon Wazirin Adamawa Atiku Abubakar wanda shi ma zai koma kananan hukumomi 3 daga 8.

Hakazalika, sake fasalin dokar ya rage wa mai martaba Sarkin Mubi, Abubakar Isa-Ahmadu, wanda ke da kananan hukumomin Michika, Madagali, Mubi ta Arewa, Mubi ta Kudu, da Maiha a karkashinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)