Kudirat Kekere Ekun ta kasance alkƙalin alƙalan Najeriya ta riƙo tun a daga watan Agusta bayan da mai shari’a Olukayode Ariwoola ya yi ritaya daga matsayin.
Tabbatar da ita kan wannan matsayi ya biyo bayan buƙatar da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya miƙawa majalisar wadda shugabanta Godswill Alpabio ya karanta.
Tinubu ya ce ya miƙa buƙatar kamar yadda sashi na 231 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya wanda aka yiwa gyara ya bawashi ikon naɗa alƙalin alƙalai bayan karbar shawara daga hukumar kula da alƙalai ta ƙasar.
Bayan tambayoyi da kuma tantancewa a ƙarshe majalisar datttawan Najeriyar ta tabbatar da naɗin Kekere-Ekun a matsayin alƙalin alƙalai ta Najeriya.
A lokacin da take bayani gaban majalisar mai shari’a Kekere-Ekun ta ce za ta rungumi aiki da fasahar zamani a ayyukan shari’a a Najeriya.
Alƙalan kotun ƙoli da na ɗaukaka ƙara na cikin waɗanda suka raka mai shari’a Kudirat Kekere Ekun majalisar dattawan Najeriya domin tantanceta da misalin ƙarfe 12:30 na yau Laraba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI