Mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin yada labarai ya sauka daga mukaminsa

Mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin yada labarai ya sauka daga mukaminsa

Jami’in ya kuma bayyana cewa ya kuma sauka daga mukaminsa na shugaban kwamitin gudanarwa tsarin da ya shafi yanani da aka sani da Project Evergreen.

A ranar 31 ga Yuli, 2023 Shugaba Bola Tinubu ya nada Ajuri Ngelale a matsayin mai magana da yawunsa kuma mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai.

Shugaban Najeriya  Bola Ahmed Tinubu Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu © Fayez Nureldine / AFP

A ranar 19 ga watan Mayun wannan shekara, shugaban ya kara masa wani nauyi a kan harkokin mulki ta hanyar nada shi wakilin shugaban Najeriya na musamman kan harkokin yanayi.

Ngelale, mai shekaru 38, a lokuta daban-daban ya kasance dan jarida mai yada labarai a gidan Talabijin mai zaman kansa na Afrika da gidan Talabijin na Channels. Ya kuma yi aiki a matsayin mai ba da shawara kan harkokin jama’a a ma’aikatar wutar lantarki ta tarayya sannan ya zama babban mataimaki na musamman kan harkokin jama’a a ofishin mataimakin shugaban kasa na lokacin Yemi Osinbajo.

A ranar 29 ga watan Mayun wannan shekara za a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban Najeriya. A ranar 29 ga watan Mayun wannan shekara za a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban Najeriya. REUTERS - JAMES OATWAY

Wasu bayyanai na dada nuni cewa jami’in ya dau wannan mataki ne sabili da zantukan da suka jibanci rashin lafaiya daga  gida, sai dai wasu yan Najeriya na ci gaba da bayyana mammakin su saukar wannan jami’in a wannan lokaci da Najeriya ke tsaka mai wuya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)