
Wani bincike da jaridar Punch, wadda ake wallafawa a ƙasar ta gudanar, ya nuna cewa ya zuwa yanzu har kungiyar masu ruwa da tsakin ta tara biliyoyin nairori domin aiwatar da ƙudirinta na tabbatar da tsaro a yankin.
Binciken ya ci gaba da cewa ‘yan kasuwar sun fara kafa ƙungiyoyi da dama na ƴan sa-kai da za su tinkari wannan matsalar.
Har ila yau binciken na jaridar ‘Punch’ ya ce a wasu ƙauyukan kudu maso-gabashin Najeriya, wasu manyan ‘yan ƙasuwa sun fara ɗaukar nauyin ƙungiyoyin ‘yan tsagera a asirce domin taka wa mayaƙan IPOB birki.
A cikin mako guda da ya wuce, jihohi a yankin kudu-maso gabashin ƙasar sun shiga cikin mawuyacin hali sakamakon hare-haren ‘yan bindiga, waɗanda su ka takura wa al’ummomin Orlu da Okigwe da Oru ta Yamma da Ihiala da sauransu.
Ana zargin kungiyar IPOB, mai fafutukar kafa ƙasar Biafra ta al’ummar Ibo zalla da wargaza sha’anin tsaro a yankin na kudu maso gabashin Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI