Shugaban Faransa Emmanuel Macron da ya gayyaci Tinubu domin ziyarar ya tarbe shi da uwargidansa Oluremi a farfajiyar fadar shugaban kasa tare da faretin sojin girmamawa, kuma wannan itace ziyarar wani shugaban Najeriya na farko a cikin shekaru sama da 20.
An dai rangada taken Najeriya da kuma Faransa domin bude ziyarar wadda ake saran ta bude kofofin fadada tatatlin arzikin kasashen ta hanyar kasuwanci da kuma zuba jari.
Shugaban Faransa Macron ya gayyaci Tinubu domin sabunta dangantaka tsakanin kasarsa da Afirka wanda ya fara tun daga shekarar 2017 da ya hau karagar mulki, a daidai kuma lokacin da aka samu juyin mulki a wasu kasashen Afirka renon Faransa, wadanda suka juyawa kasar baya.
Faretin ban girmar da aka yiwa Tinubu a Paris © Michel Euler / ReutersMacron ya bayyana wannan ziyarar a matsayin wadda zata bada damar inganta alaka tsakanin Faransa da Najeriya, musaman la'akari da matsayin kasar wadda itace ta farko a arzikin man fetur a Afirka, kana kuma tayi fice wajen fina finan Nollywood.
Sai dai kasar na fuskantar matsalolin koma baya da suka hada da matsalar tsaro da kuma cin hancin da ya jefa mutane miliyan 129 cikin talauci da rayuwa kasa da dala 2 kowacce rana.
Wannan ziyara na da matukar tasiri ga Najeriya wadda a halin yanzu ke fama da hauhawan farashin kayyaki da kuma abinci, saboda kofar da zata bude na kulla wata sabuwar dangantaka tsakanin 'yan kasuwar kasar da na Faransa tare da bude kofofin zuba jari.
Tinubu da Macron AP - Michel EulerA wannan ziyara, Najeriya na fatar ganin ta kulla yarjeniyoyi a bangaren noma da tsaro da ilimi da lafiya da matasa da kuma makamashi, kamar yadda ofishin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar.
Ana kuma saran Tinubu da Macron su tattauna muhimmancin dangantakar al'adu da ma'adinan karkashin kasa da kasuwanci da zuba jari tare da sadarwa.
Najeriya mai yawan mutanen da suka zarce miliyan 220 na zama babbar kasuwa ga manyan kasashen duniya dake sarrafa kayayyaki, duk da matsalolin da suka yiwa kasar dabaibayi irin su tsaro da kuma cin hanci da rashawa.
Katsewar hulda tsakanin Faransa da wasu kasashen da ta rena irin su Nijar da Burkina Faso da kuma Mali da sojoji suka kwace mulki, zai bata damar maye gurbinsu da Najeriya, babbar kasar dake sahun gaba wajen tattalin arziki a Afirka.
Faransa na Shirin fadada irin wannan dangantaka lokacin da za ta dauki nauyin taron ta da shugabannin Afirka da zai gudana a shekarar 2026, inda take fatar samun dama a wasu kasashe irin su Kenya da Zambia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI