Ma'aikatar tsaron Najeriya ta gargaɗi masu fatan juyin mulki a ƙasar

Ma'aikatar tsaron Najeriya ta gargaɗi masu fatan juyin mulki a ƙasar

Wata sanarwa ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labarai na shelkwatar tsaron ƙasar, Birgediya Janar Tukur Gusau ta bayyana ƙarara cewa rundunar sojin Najeriya ta mayar da hankali ne ga ainihin aikin da kundin tsarin mulkin ƙasar ya shata mata, waɗanda su ka haɗa da tsare mutunci da ƙimar ƙasar, tare da tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Gusau ya ce ƴar ƙwarya-ƙwaryar zaman lafiya da aka samu a ƙasar ta tabbata ne sakamakon gudummawa da goyon bayan da shugaba Tinubu ya ke bai wa rundunar sojin da kuma irin sadaukarwar da jagorancin rundunar ke yi.

Ya kuma tabbatar wa da ƴan Najeriya cewa rundunar sojin, tare da hadin gwiwar  sauran hukumomin tsaro za su ɗauki matakan da su ka dace wajen kawar da duk wani yunƙuri na yi wa kundin tsarin mulki ƙasar karan tsaye.

Sanarwar ta shalkwatar tsaron na zuwa ne a yayin da ake bayyana damuwa game da wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta na wani gungun mutane da ke yin magiya ga sojojin da ke cikin wani ayarin motoci su yi juyin mulki a ƙasar ko za a samu sauƙin rayuwa.

Ba wannan ne karon farko da ake samun masu irin wannan kiraye-kiraye ba, don a duk lokacin da ka yi kiciɓis da masu korafi kan tsadar rayuwa, zai yi wuya ba a ji makamancin wannan kira ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)