
A sakon da ya wallafa, El Rufai wanda ya ce yanzu haka ya na kasar Masar, ya ce zai koma Nijeriya a ranar 20 ga wannan watan, kuma ba shi da wata fargaba.
Tsohon gwamnan ya kuma ƙara da cewar yanzu ne zai ɗauki dogon lokaci ya na zama a cikin ƙasar saɓanin yadda yake yi a baya.
El Rufai ya yi zargin samun saƙonnin barazanar da aka yi ta hannun abokansa, iyalansa da kuma abokan tafiyar siyasarsa da dama, saboda ganin sun sa shi tserewa daga Nijeriya domin samun mafaka a ƙasashen ƙetare.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewar ya jingine shirin neman iliminsa, domin mayar da hankali akan manufar da ya sa a gaba, tare da cewar lokacin shiru ya wuce.
El Rufai ya ce kamawa da tsarewa da kuma azabtar da abokan adawar siyasa ba wani sabon abu ba ne a rayuwa, saboda an taɓa tsare shi har sau 3 a baya saboda bayyana ra'ayoyinsa akan gwamnatocin da suka gabata.
Saboda haka, tsohon gwamnan ya ce kame da azabtarwar ba wani sabon abu bane, kuma Allah kadai ke sanyawa Bil Adama lokacin barin duniya.
El Rufai ya shaidawa mutanen da ya ce basa bacci duk lokacin da yake Nijeriya da su ƙwan da sanin cewar yana kan hanyar komawa kasar domin halartar bikin ƙaddamar da littafin tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Babangida da za'ayi a ranar 20 ga watan nan.
Tsohon gwamnan ya ƙarƙare da cewar su ga Allah kadai suka dogara, kuma basa tsoron wani mahaluki wanda ba Allah bane, yayin da ya ce fatar su ita ce samun makoma ta gari, amma kuma su kan shiryawa fuskantar akasin haka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI