Lauyoyi a Najeriya sun maka gwamnati kotu kan rikicin 'yan gudun hijirar Benue

Lauyoyi a Najeriya sun maka gwamnati kotu kan rikicin 'yan gudun hijirar Benue

 Darakta mai kula da sashin shari’a na kungiyar, Barista Bamidele Jacobs, ya ce makasudin shine a tabbatar da cewa an bi muhimman hakkokin wadanan yan gudun hijira.

Barista Bamidele Jacobs ya karasa da cewa, “sun shigar da karar ne kamar yada kudin tsarin mulkin Najeriya ya yi tanadi ta shekara ta 1999, da kuma dokar ‘yancin dan Adam ta Afrika da kasashe suka rattabawa hannu.

Wani daga cikin sansanin yan gudun hijira a Najeriya Wani daga cikin sansanin yan gudun hijira a Najeriya Ute Grabowsky/Photothek via Getty Images

Barista Bamidele Jacobs ya na mai cewa “shari’ar ta nuna wajibcin da ya rataya a wuyan gwamnatin tarayyar Najeriya na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasarta, musamman ‘yan gudun hijira a jihar Benue kamar yadda yake kunshe a sashin kudin tsarin mulkin wannan kasa,wanda ya tabbatar da yancin rayuwa, mutuncin dan adam, da ƴancin kai. “Bugu da kari, sharuddan 4, 5, 6, 16, 22, da 24 na yarjejeniya da ta shafi yancin Dan Adam da Jama’a na Afirka sun ba da umarnin cewa dole ne gwamnati ta samar da tsaro tare da tabbatar da mafi kyawun yanayin lafiyar jiki da ta kwakwalwa ga daukacin ‘yan kasar.

 A karshe dai lauyoyin sun  nuna rashin jin dadinsu ganin ta yada wadanan yan gudun hijira ke rayuwa a wadanan wurare, ga cunkoson jama’a, rashin tsaftar muhalli, rashin isasshen tsaro, jama’a na kamuwa da cututtuka, wadanda suka yi illa ga mata da kananan yara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)