Kuskure ne cire hannun Babban Hafsan tsaro wajen sayen makamai - Sanata Lawal

Kuskure ne cire hannun Babban Hafsan tsaro wajen sayen makamai - Sanata Lawal

Sanata Lawal ya ce yana da matukar muhimmanci a sanya hannun babban hafsan da kuma ma'aikatar tsaro cikin sayen kayan sojin maimakon watsi da su.

Tsohon shugaban Majalisar wanda ke jawabi ga taron manyan kwamandodin dake gudanar da aikin samar da zaman lafiya a sassan kasar tare da shugabannin hukumomin tsaro na kasa, ya ce ya gamsu da rawar da wadannan manyan jami'ai ke takawa a yunkurin su na tabbatar da zaman lafiya, yayin da ya shaida musu cewar Majalisar tarayya za ta ci gaba da basu goyan baya wajen gudanar da ayyukan su.

Har wa yau, ya janyo hankalin kwamandodin akan muhimmanci aikin tare da kuma musayar bayanan asiri a tsakanin su.

Taron kwamandodin tsaron najeriya tare da manyan hafsoshin tsaron kasa a Abuja Taron kwamandodin tsaron najeriya tare da manyan hafsoshin tsaron kasa a Abuja © Sanata Ahmed Lawal

Sanata Lawal ya jinjinawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu saboda kara yawan kudaden aiki ga bangaren tsaro a kasafin kudin wannan shekara to tabbatar da tsaron kasa.

Najeriya na fama da dimbin matsalolin tsaron da suka hada da mayakan boko haram da 'yan bindigar dake satan shanu da kuma garuwa da mutane da masu fasa bututun mai da tare da masu fafutukar kafa kasar Biafra.

Masana harkar tsaro na bayyana cewa sanya ofishin babban hafsan tsaron zai taimaka wajen sanya ido da kuma dakile wasu kura kuran da ake samu wajen sayo kayan aikin sojin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)